EFCC ta kai samame wani wuri sayar da motoci inda ta kwace motoci 29


Ofishin hukumar Yaki Da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati EFFC dake jihar Lagos ya kai samame wani wajen dillancin motoci dake jihar mai suna Astrax Auto Shop.

Samamen ya biyo bayan rahoton bayanan sirri da hukumar ta samu kan aiyukan masu wurin sayar da motocin waɗanda ake zargi da aikata zambar kudade ta intanet.

Mai rikon mukamin jami’in hulda da jama’a na hukumar ya ce bincike kan ayyukan gungun mutanen da suka kware wajen satar bayanan Imel a kasar Amurka ya nuna cewa suna tura abin da suka samu zuwa wasu asusun bankuna na abokan taadar tasu dake ƙasar Amurika.

Ya ce mutanen suna turo kudaden ta hanyar sayen motoci da aka yi gwanjonsu a Amurka su kuma turo Najeriya.

Motocin da hukumar ta EFCC ta kama a wurin sun hada da Toyota Corolla (4); Toyota Camry (7); Toyota Highlander (2); Toyota Venza (2); Range Rover (2); Ford SUV (1); Mercedes Benz (3); Toyota 4runner (1); Toyota Sienna (1) ; Honda Accord (4); Toyota Sequoia (1) da kuma Kia (1).

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like