EFCC ta kai samame gidan Yari


Jami’an hukumar EFCC mai yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati sun kai samame gidan tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulzaziz Yari dake Talata-Mafara da yammacin ranar Lahadi.

Ibrahim Dosara,mai magana da yawun tsohon gwamnan shine ya tabbatar da faruwar haka a wata tattaunawa da kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN.

“Gaskiya ne jami’an hukumar EFCC sun kasance a gidan mai girma tsohon gwamna dake Talata Mafara a jiya Lahadi,” ya ce.

“Maigidana yana da masaniyar zuwansu sun samu damar bincikar dukkanin dakuna da kuma ofisoshi sun tafi bayan shafe sa’o’i da dama suna bincike.”

Wani mutum da ya ganewa idonsa abin da ya faru ya fadawa NAN cewa jami’an na EFCC sun isa gidan da misalin karfe 06:00 na yamma cikin tsauraran matakan tsaro inda suka rufe kofofin shiga gidan ta gaba da baya.

Ya ce sun umarci wadanda suke cikin da su tsaya a inda suke ya yin da suka hana kowa shiga ciki.

Ya kara da cewa jami’an na EFCC ba su fito daga gidan ba sai kusan karfe 11 na dare dauke da wasu jakunkuna da basu san meye a ciki ba.

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like