EFCC ta kai samame gidan Ambode


Jami’an hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati sun kai samame gidan tsohon gwamnan jihar Lagos,Akinwumi Ambode ranar Talata.

Mai magana da yawun EFCC, Tony Orilade ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce hukumar dake yaki da cin hancin ta karbi korafi akan tsohon gwamna Ambode kuma ta fara binciken gwamnatinsa.

“Mun karfi korafi game da gwamnan kuma muna bincikensa,” ya ce.

Da aka tambaye shi ko jami’an hukumar sun je gidan tsohon gwamnan sai ya ce ” Eh wani bangare ne na binciken.”

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like