EFCC ta gano gidaje biyu mallakin Jang


Hukumar EFCC dake yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati ta gano wasu gidaje mallakin tsohon gwamnan jihar Plataeu,@Jonah Jnda da darajar su ta kai miliyan ₦500.

Mai rikon muƙamin kakakin hukumar, Tony Orilade shine ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

A cewar sanarwar, gidajen sune masu lamba ta 8 da 9 dake kan titin Gobarau a rukunin gidajen gwamnati dake Unguwar Rimi a Kaduna.

Orilade ya ce binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa an saya gidajen ne daga kamafanin New Capital Properties Limited, wanda wani bangare ne na kamfanin Northern Nigerian Development Company (NNDC) Kaduna.

Jang na fuskantar tuhume-tuhume 12 a gaban kotu da suka hada da karkatar da kudaden jama’a.

An gurfanar da shi a gaban kotun tare da wani mutum mai suna Yusuf Pam wanda tsohon jami’in gwamnati ne a jihar.

Comments 2

Cancel reply

Your email address will not be published.

You may also like