EFCC ta fara rufe wasu kadarori dake da alaka da Rochas


Jami’an hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa sun rufe wasu kadarori da aka gano suna da alaka da Rochas Okorocha tsohon gwamnan jihar Imo.

A wata sanarwa da aka fitar ranar Laraba,Tony Orilade mai magana da yawun hukumar ta EFCC ya ce hukumar ta sawa alama a kadarorin dake da alaka da gwamnan da kuma makusantantan shi kan kin amsa gayyatar hukumar da ya yi domin ya amsa tambayoyi.

Kadarorin da abin ya shafa sun hada da Otal, makarantu, rukunin gidaje, babban shagon sayar da kayayyaki da kuma gidaje.

Orilade ya ce sun fara yiwa kadarorin alamar rufewa bayan da suka shafe tsawon lokaci suna gudanar da bincike.


Like it? Share with your friends!

1
72 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like