Hukumar EFCC ta kama Abdon Dalla mai bawa gwamnan jihar Bauchi,Bala Muhammad shawara kan harkokin ma’aikata da kuma kwadago bisa zargin sayan kuri’a.

An kama Dalla a ranar Asabar jim kaÉ—an bayan da ya kada kuri’a a zaben cike gurbi da aka gudanar a karamar hukumar Dass ta jihar.

Da yake magana da manema labarai bayan faruwar lamarin, shugaban karamar hukumar,Sulaiman Muhammad ya ce kudin da aka samu ba na bai da shawarar bane kudi ne da za a rabawa wakilan jam’iyar dake bakin akwati.

Muhammad ya ce an kama Dalla jim kadan bayan kada kuri’a da kuma ganawa da manema labarai.