EFCC ta buɗe asusun ajiyar gwamnatin jihar Benue


Hukumar Yaki Da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati wato EFCC ta bude asusun ajiyar gwamnatin jihar Benue da ta rufe.

Mai magana da yawun gwamnan jihar, Terver Akase shine ya tabbatar da haka cikin wata tattaunawa da ya yi da gidan Talabijin na Channels a ranar Alhamis.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa EFCC ta rufe asusun ajiyar gwamnatin jihar Benue ranar Talata.

Akase ya yi allawadai da matakin inda ya ce ba dai-dai bane akawo wa jihar na kasu ta fannin hada-hadar kudade saboda matsalar tsaro da jihar ke fama da ita.

“Idan EFCC ta rufe asusun ajiyar kowace gwamnatin jiha, Benue ko wata jihar daban ina tunanin hakan ya sabawa kundin tsarin mulki.ba dai-dai bane saboda karufe ayyukan gwamnati gaba ɗaya.

“Dole gwamnati ta kashe kudi, musanman jihar Benue inda ake da matsalar tsaro.”


Like it? Share with your friends!

1
77 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like