EFCC Ta Ba Ma’aikatar Cikin Gida Shawara Kan Masu Cuwa-cuwar FasfoABUJA, NIGERIA – Hukumar EFCC ta ja hankalin ma’aiktar cikin gida da ta harkokin waje da su bullo da dabarun tsaftace ayyukansu na yin fasfo don magance matsalar buga fasfo din ta bayan gida.

Matsalolin da ake fuskanta game da samar da fasfo ko sabuntawa ta bayan fagge tare da karbar makudan kudadde daga hannun masu bukata musamman na gaggawa su na ci gaba da yawaita.

Hakan ne ya sa ma’aikatar harkokin cikin gida ta yi kira ga hukumar EFCC da ta fara kamen wadanda ke da hannu cikin al’amarin bisa la’akari da korafe-korafen da ‘yan Najeriya ke yi a game da mawuyacin yanayin da suke shiga wajen neman sabo ko sabunta fasfo a kan lokaci da suke bukata.

Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa (Instagram/EFCC)

Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa (Instagram/EFCC)

Jinkirin da ake samu a sha’anin samar da fasfon dai a cewar hukumomin da abin ya shafa, baya rasa nasaba da tasirin bullar annobar korona birus a karshen shekarar 2019 da ta tsayar da alamurran yau da kullum a fadin duniya, inda aka sami karancin takardun buga fasfo, lamarin da ya kai ga ma’akatar sha’anin cikin gida da ma hukumar kula da shige da fice tara tulin takardar neman fasfon ‘yan kasa a ciki da ma wajen Najeriya.

To sai dai wasu bayanai daga wasu da suke da masaniya kan harkar sun ce, matsalar ta samo asali ne saboda matakin da gwamnatin Shugaba Muhamamdu Buhari ta dauka na dakatar da wata kwangila da aka bayar tun zamanin gwamnatin Obasanjo, inda wani kamfanin kasar waje ke bugawa Najeriya takardar fasfo. Lamarin da ya kai ga samun sabani har kamfanin ya ce sai gwamnati ta bashi kudi hannu kafin ya buga mata takardun fasfo, abin da ya sa ke nan ake samun karancin takardun fasfo din.

‘Yan Najeriya daga ciki da wajen kasar dai sun yi ta korafe-korafe a kan yanayin da suka shiga sakamakon tsawon lokacin da ake dauka wajen buga sabo ko sabunta tsohon fasfo kamar yadda Trust Idiong, wani dan kasar da ya yi jiran kusan watannin 5 a yayin neman sabunta fasfo dinsa al’amarin da ya kusa sanya shi rasa damar rubuta jarabawar shara faggen zuwa kasar waje Karatu na IELTS.

Jami'an Hukumar EFCC

Jami’an Hukumar EFCC

A makonnin baya-bayan nan ma sai da majalisar wakilai ta kasar ta kuduri aniyar gudanar da bincike kan badakalar fasfo, karancin takardun bugawa da kuma jinkirin da ake samu wajen bayarwa daga bangaren hukumar shige da fice ta Najeriya.

Haka shi ma ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya taba jadada kokarin da ma’aikatarsa ke yi wajen samo bakin zaren kan al’amarin, inda ya bukaci yan kasa su kwantar da hankalinsu yana mai cewa akwai isassun takardun yin fasfo a yanzu kuma an tura su ga ofisoshin hukumar don biyan bukatun yan Najeriya.

Duk kokarin ji ta bakin hukumar shige da fice ta Najeriya a yayin hada wannan rahoton ya ci tura.

Saurari rahoto cikin sauti daga Halima Abdulrauf:


Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg