(DUNIYA): Faransa Ce, Silan Talauci A Afrika – Italiya


Ministan tattalin arzikin kasar Italiya, Luigi di Maio, ya zargi kasar Faransa da zama ummul’aba’isin talaucin dake addabar kasashen Afrika.

Mista Maio, ya ce kamata ya yi kungiyar tarrayyar turai ta kakaba wa Faransa dama sauren kasashe kamar Faransar dake talauta Afrika takunkunmi, wanda hakan ne yake sa mutanen Afrikar barin kasashensu, saboda a cewarsa kamata ya yi ‘yan AFrika su zauna Afrika, ba wai a tekun mediteranien ba.

Ya kara da cewa, idan mutanen Afrika suna barin kasashensu a yau, saboda kasashen turai, musamman faransa, har yanzu basu kawo karshen mulkin mallakar gomman kasashen Afrika ba ne, sannan ya ce ba dan Afrika ba, Faransa bata isa ta zo a jerin kasashen duniya mafiya tattalin arziki ba.


Like it? Share with your friends!

-1
72 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like