Dukkanin yan Najeriya za su iya fadawa cikin talauci matukar ba dauki mataki ba -Atiku


Atiku Abubakar dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyar PDP a zaben shekarar 2019 ya ce idan har ba a dauki mataki ba to baki dayan mutanen Najeria za su fada cikin kangin talauci.

Da yake mayar da martani kan rahoton hukumar Majalisar Dinkin Duniya (MDD) dake lura da cigaban kasashe UNDP dake cewa yan Najeriya miliyan 98 ne suke rayuwa cikin matsanancin talauci,Atiku ya ce ko da Aliko Dangote mutumin da yafi kowa kudi a nahiyar Afirka shima matsalar talaucin dake cigaba da mamaye Najeriya yaa shafe shi.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya zargi wadanda suka jefa Najeriya cikin halin da take ciki da yin ko inkula da batun inda ya kara da cewa babbar matsalar tsaron da take addabar kasarnan ba Boko Haram ba ce ko kuma yan bindiga masu kashe mutane fa ce yadda ake jefa jama’a cikin talauci da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin kasarnan.

Ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su hada hannu domin lalubo mafita kan batun.


Like it? Share with your friends!

-1
103 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like