Duk ma’aikacin da baya cikin tsarin IPPIS ba zai sake samun albashi ba – Ministar kudi


Duk wani ma’aikacin gwamnatin tarayya dake karkashin wata ma’aikata ko hukumar gwamnati da baya cikin tsarin biyan albashi na bai daya watau, IPPIS-Integrated Payroll and Personnel Information System ba zai sake samun albashinsa ba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito ministar kudi, kasafin kudi da tsare tsare, Zainab Shamsuna Ahmad ce ta bayyana haka yayin da take gabatar da jawabi game da tsare tsaren kashe kudi na gwamnatin tarayya na matsakaici zango a Abuja, inda tace dokar za ta fara aiki ne daga watan Oktoba.

Majiyarm ta ruwaito ministan ta bayyana cewa wannan mataki ya zama wajibi domin toshe duk wasu ramuka da kudaden da gwamnati suke bi suna bacewa, tare da kokarin rage kudaden ayyukan yau da kulluma da gwamnati ke kashewa.

“Kudaden da ake kashewa a kan ma’aikata da yan fansho ya haura naira tirilyan 3, kuma kara hauhawa yake yi, amma gwamnati na daukan matakan rage wannan tashin gwauron zabi da kudaden suke yi, daga ciki akwai umarnin shugaban kasa na cewa daga watan Oktoba na 2019 dukkanin ma’aikatu da hukumomi sun shigar da ma’aikatansu tsarin IPPIS.” Inji ta.

Haka zalika ministar ta ce nan bada jimawa ba gwamnatocin jahohi zasu fara biyan kudin tallafi da gwamnatin tarayya ta basu a shekarar 2016, saboda a cewarta kudaden mallakin babban bankin Najeriya, CBN ce, don haka za’a cire daga kudadensu na wata wata da gwamnatin tarayya ke basu.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like