Duk Gwamnan APC Da Bai Biya Albashin Ma’aikata Ba, Kada Ku Sake Zaɓen Sa – Buhari


Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya shawarci ya shawarci ‘ƴan Najeriya da Kada su sake su zaɓi duk wani baragurbin shugaba ya koma kan kujerar mulki ko da kuwa a jam’iyyarsa ta APC yake takara. Inda ya kawo misali da ire-iren gwamnonin da suka kasa biyan albashin ma’aikatan jiharsu amma kuma sun sake fitowa takara don su sake hayewa kan muƙamansu na gwamna a karo na biyu. A cewarsa mai kamar zuwa akan aika. Kuma juma’ar da za ta yi kyau da Laraba ake gane ta. Don haka ya yi kira ga masu zaɓen da su duba cancanta yayin da za su kaɗa ƙuri’unsu a kakar zaɓe ta 2019 mai zuwa.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi cikin harshen Hausa tare da gidan rediyon Muryar Amurka (VOA) wanda ya gudanar a safiyar yau Talata.

Buhari ya ƙara da cewa, yana mamakin yadda irin waɗannan Gwamnoni suke ƙin biyan ma’aikatan jihohinsu haƙƙoƙinsu duk kuwa da sun riga sun karɓi kason jiharsu daga aljihun gwamnatin tarayya. Kuma yana mamakin ma yadda waɗannan gwamnoni suke iya runtsawa su yi bacci alhali ba su sauke haƙƙin ma’aikatan jiharsu ba. A cewarsa; “Su ma fa waɗannan ma’aikatan suna da iyalansu da suke karkashin kulawarsu kuma za su biya kuɗin haya, su biya kuɗin makarantar yaransu, da kuɗin asibiti ga kuma uwa uba ci da sha”.

Ya ƙarƙare da cewa, kundin mulkin ƙasar nan ya bai wa kowanne Gwamna dama a kan yadda zai kashe kuɗin ƙasarsa ba tare da an sa masa ido ba. Wannan ya sa wasu shugabannin suke amfani da wannan damar su handame kuɗaɗen ba tare da sun yi wa kama’a aiki ba. Don haka ya yi kira ga talakawa da su yi amfani da damarsu ta zaɓe don su zaɓi shugabanni na ƙwarai.

A lokacin da aka yi masa tambaya a kan yaƙi da cin hanci da rashawa da gwamnatinsa take iiƙirarin tana yi. Buhari ya kada baki ya ce ai yanzu ba kamar da ba ce. Yana gudanar da yaƙin a cikin siyasa ne da dabara. Shi ya sa ma ake ganin kamar ba ya sauri, amma da sannu za a ga sakamako.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like