Daya daga cikin manyan Malam Addinin Musulunci Shiekh Dakta Bashir Aliyu Unar Alfuqan, ya yi fashin baki game da yin sakin aure a cikin wasan kwaikwayo (fim).

Dakta Bashir Alfurqan, ya ce dukkan wani dan wasan fim da ya furtawa matar sa ta ciki shirin fim saki, to babu shakka matar sa ta gida ya saka.

Babban Shehin Malamin ya ce babu wasa a sakin aure, indai ka sake ka furta saki a wasan kwaikwayo, to lallai matar ka ta gida ka saki babu shakka a kan wannan.

Malam Bashir Aliyu, ya tabbar da hakan ne lokacin da yake gudanar da karatu a masallacin Alfurqan, kunshe cikin wani faifayin bidiyo da Jaridar Dimokuradiyya take da shi.

Idan baku manta ba masana’antun shirya finafinan misali kamar Kannywwod, sukan shirya fim har ma a daura aure wani lokaci har da saki, to lallai Malam ya ce babu wannan a Musulunci, dukkan wanda ya saki matar sa ta cikin shirin fim, to matar sa ta auren sunna ya saka.