Duk Da Hukuncin Kotu, Har Yanzu Shugaban Ƙaramar Hukumar Suleja Bai Kama Aiki Ba


A ranar 12 ga watan Maris ta wannan shekarar, Kotun sauraren korafin zaben Kananan Hukumomi da ke zama a birnin Minna, ta Jihar Neja, ta sauke nasarar zaben Hon. Hussaini Ladan na Jam’iyyar APC Mai Mulki a matsayin zababben Shugaban Karamar Hukumar Suleja.

A nan take kuma kotun ta bayar da umurni ga Hukumar Zabe ta Jihar Neja da ta hanzarta mika takardar Shaidar nasarar zabe ga Adamu A Usman na Jam’iyyar PDP kuma a rantsar da Shi nan take.

A hukuncin da su Ka yanke, Alkalai su uku, sun ce; “Baki dayan Mu mun yarda da korafin Mai karar akan cewa Wanda a ke tuhuma tare da Jam’iyyar APC sun Shiga takarar kujerar Shugaban Karamar Hukumar Suleja ba tare da sahihin dan takarar kujerar Mataimakin Shugaban Karamar Hukuma ba. Haka kuma ya saba wa sashe na 33 da 36 na kundin tsarin dokar zabe da aka sabunta a shekarar 2010 na Hukumar Zabe mai zaman kanta ta Jihar Neja yayin da ita kuma Jam’iyyar APC ta saba da wannan tsarin inda ta sauya sunan Hon. Zakari Isah a zaben Kananan Hukumomi na shekarar 2019 a Jihar Neja kamar yadda ya faru a misalin shara’ar PDP da sauran su da Biobarakuma Degi-Ermienyo da wasun su, Mun zartar.”

Sun kuma bayar da umurnin tabbatar da Adamu Usman na PDP a matsayin Wanda ya lashe zaben kananan hukumomi na ranar 30 ga watan Nawamba, 2019 a Karamar Hukumar Suleja.

Nan take kuma kotun ta umurci Hukumar Zabe Mai zaman kanta da ta gaggauta mika takardar Shaidar nasarar lashe zabe ga Adamu Usman.

Jam’iyyar APC da dan takarar ta Hon. Hussaini Ladan sun daukaka wannan hukunci da kotun sauraren korafin zabe ta zartar, a lokaci daya kuma, Dan Jam’iyyar Hon. Abdullahi Maje ya bi bayan Jam’iyyar da Hussaini Ladan wurin shiga daukaka karar sakamakon shima yana cikin shara’ar. Kuma kotun ta saurari Hon. Abdullahi Maje da Jam’iyyar APC yadda ya kamata. Sannan a ranar 15 ga watan Yuni, 2020 Kotun daukaka karar ta kori karar na Hon. Hussaini Ladan, Jam’iyyar APC da Hon. Abdullahi Shuaibu Maje sabo da rashin hujjoji da za su gamsar da kotun domin ta sauya wancan hukunci da kotun sauraren korafin zabe ta zartar.

Sanin kowa ne cewa; duk wani korafin zabe na Kananan Hukumomi na karewa ne a kotun daukaka kara da Jiha ta kafa domin zabe.

Tun tsawon Wannan lokaci, Hukumar Zabe ta Jihar Neja karkashin Jagorancin Alhaji Baba Aminu na wasan ‘Yar boye tsakanin ta da Dan takarar Jam’iyyar PDP Wanda kotu ta bayar da umurnin Hukumar ta ba shi takardan nasarar lashe zabe. Har izuwa yau ba Hukumar zaben ba ta yi biyayya ga umurnin kotu ba.

Wakilin mu ya yi kokarin jin ta bakin Shugaban Hukumar Zaben, ya ce a zo ofishin su za a samu duk bayani da ake son a ji daga bakin Sakataren Hukumar dangane da wannan batu na Karamar Hukumar Suleja.

Sakataren Hukumar, Habibu Bobi ya yi alkawari mu ba shi lokaci zai kira mu amma har izuwa wallafa Wannan rahoto bai kira ba kuma ba ya amsa kiran mu.

A na ta bayanin, Mai Magana da yawun Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello, Mary Noel Berje ta ce; “Ita Wannan batu bai shafeta ba, magana ce ta Jam’iyya.”

Idan masu Karatu za su tuna, makamancin irin haka ya faru a hukuncin da kotu ta yanke na batun kafin zabe a Karamar Hukumar Magama, Haka wannan hukumar zaben ta bijirewa umurnin Kotu, har sai da Babban kotu a Jihar Neja ta yi yunkurin aikawa da Jami’an Hukumar gidan Yari dalilin bijirewa umurnin Kotu. Amma duk da haka sai da a Ka yi watanni hudu cur kafin su bi umurnin na kotu. A halin yanzun babu Shugaban Karamar Hukuma a kujerar Karamar Hukumar Suleja


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like