Lamarin ya faru ne a daidai dai dai sabon Wuse dake yankin karamar hukumar Tafa a jihar Nejan.

Bayanai dai sun nuna cewa zanga-zangar ta rikide zuwa tarzoma kuma an shirya ta ne domin nuna takaici akan yadda ‘yan bindiga ke ci gaba da sace mutane domin neman kudin fansa a yankin.

Zanga-zangar Nuna Takaicin Rashin Tsaro A Jihar Nejan Najeriya

Zanga-zangar Nuna Takaicin Rashin Tsaro A Jihar Nejan Najeriya

Daya daga cikin masu zanga-zangar ya ce suna bukatar a sako masu sama da mutum 50 da aka sace masu a ranar Lahadi 23 ga watan Mayu.

Gwamnatin jihar Nejan dai ta ce tana sane da wannan zanga-zanga kuma tana daukar matakai akan matsalar rashin tsaron, in ji Sakataren Gwmnatin jihar Nejan Alhaji Ahmed Ibrahim Matane.

Zanga-zangar Nuna Takaicin Rashin Tsaro a Jihar Nejan Najeriya

Zanga-zangar Nuna Takaicin Rashin Tsaro a Jihar Nejan Najeriya

Zanga-zangar dai ta kai ga kona ofishin ‘yan sanda a yankin, sai dai har ya zuwa Lokacin hada wannan rahoto rundunar ‘yan sandan jihar ba ta ce komai ba, kuma kokarin samun kakakin ‘yan sandan Wasiu Abiodun ya ci tura.

Amma Sakataren Gwamnatin jihar Nejan Ahmed Matane ya ce za su hukunta masu daukar doka a hannunsu.

Saurari rahoto cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari: