DSS ta samu yardar kotu Na Tsare Sowore har tsawon kwanaki 45


Da yake yanke hukunci a ranar Alhamis, 8 ga watan Agusta, Justis Taiwo Taiwo, yace zai bari hukumar ta tsare Sowore na tsawon kwanaki 45 a karon farko, wanda ana iya sabonta shi idan an nemi hakan, domin ba DSS damar kammala bincikenta.

A karar da DSS ta shigar, karkashin sashi na 27 na dokar hana ta’addanci, hukumar ta zargi Sowore da aikata ta’addanci.

Ta kuma gabatar da faifan bidiyo biyu, wanda ke dauke da rikodin haduwar Sowore da Nnamdi Kanu, Shugaban kungiyar masu fafutukar neman yankin Biyafara da kuma wata hira inda Sowore yace mamboin kungiyar Shi’a ma za su hada hannu da shi wajen durkusar da gwamnatin Najeriya.

hukumar DSS masu fararen kaya a jihar Edo sun kama wasu mutum biyu da a ke zargi da yin shiga a matsayin Mai dakin shugaban kasan Najeriya watau Hajiya Aisha Buhari.

Haka zalika kuma an kama wani mutumi da ke amfani da sunan mataimakin shugaban kasa watau Farfesa Yemi Osinbajo.

Mun samu wannan labari ne a Ranar 7 ga Watan Agusta, 2019. Mataimakin Darektan hukumar na DSS a Edo, Galadima Byange, shi ne ya gabatar da wadannan wadanda a ke zargi da laifi masu suna Amos Asuelimen da Kelvin Ogashi a Garin Benin jiya.


Like it? Share with your friends!

1
77 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like