DSS: Elzakzaky na nan da ransa


Hukumar tsaro ta farin kaya DSS a ranar Juma’a tace shugaban Kungiyar Yan’uwa Musulmi ta Najeriya wacce akafi sani da shi’a Ibrahim Elzakzaky yananan da ransa.

Wani ma’aikacin hukumar da ya nemi a boye sunansa shine ya shedawa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN cewa Elzakzaky na cikin koshin lafiya.

Rundunar sojin Najeriya har yanzu taki mayar da martani kan rohatannin dake cewa shugaban kungiyar ta shi’a ya mutu.

Mai magana da yawun rundunar Sani Usman wanda jaridar The Cable ta tuntuba ya gaza daga wayarsa ko kuma bada amsar gajeren sakon da aka tura masa kan lamarin.

Yan kungiyar ta shi’a sun shafe watanni suna gudanar da zanga-zangar kira da a saki shugaban nasu wanda ke tsare a hannun jami’an tsaro tare da maidakinsa tun shekarar 2015.

Sai dai jami’an tsaro sun sha nanata cewa suna cigaba da tsare shine domin tsaron lafiyarsa.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like