Donald Duke ya lashe tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyar SDP


Toshon gwamnan jihar Cross River Donald Duke ya lashe tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyar SDP a zaɓen shekarar 2019.

An bayyana tsohon gwamnan a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin na ranar Lahadi a wurin babban taron jam’iyar da aka gudanar a filin Old Parade Ground dake Abuja.

Abdul Ishaq jami’in tattara sakamakon zaben ya ce Duke ya samu ƙuri’u 812 inda ya kayar da a tsohon ministan yada labarai, Farfesa Jerry Gana wanda ya samu ƙuri’u 611.

Isiaq ya ce John Dara ya samu ƙuri’u 104, Iyorwuese Hagher ya samu ƙuri’u 72 yayin da Felix Osakwe ya samu ƙuri’u 10 aka kuma soke kuri’a 60.

A jawabinsa na nasarar da ya samu,Duke ya ce zamansa dan takara nasara ce ga dukkanin yan takarar da suka shiga zaben fidda gwanin.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like