DOLE SAI GANDUJE YANA WAJEN ZAI ZO MAJALISA – Inji Wanda Ya Dauki Bidiyo


Wanda ya dauki bidiyon Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje yana karbar dalolin Amurka yayi alkawarin zai bayyana agaban kwamitin binciken gwamna domin tabbatarwa da mutanen Jihar Kano da duniya cewa ba sharri aka yiwa Gwamna ba.

Sai dai shi wannan bawan Allah da har yanzu ba’asan ko waye ba yace sai anyi masa abubuwa guda shida kamar haka:

1. Dole sai gwamna Ganduje ya bayyana a ranar da shima zaizo babu maganar turo wakili.

2. Dole sai mawallafin jaridar Daily Nigerian wato Jaafar Jaafar shima yazo.

3. Dole sai Kwamandan Hisbah ta jihar Kano Mallam Aminu Ibrahim Daurawa shima yazo

4. Dole sai an gayyato kwararru wadanda suka San bidiyo Daga kasashen waje domin suzo tantantance a ranar.

5. Dole sai an bashi tabbacin baza’a bayyanashi a idon duniya ba kowa yasan waye.

6. Dole sai kwamitin binciken ya tabbatar da zai bashi kariya ranar da zaizo majalisar.

Wannan sharadi daya bayar suna kunshe cikin wata takarda daya aikewa majalisar a jiya.

Yanzu dai abinda ake jira a gani shine abinda majalisa zatace akan wannan cigaba da aka samu.


Like it? Share with your friends!

-1
139 shares, -1 points

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like