Dogara ya rantsar da dan majalisar wakilai na jam’iyar APC daga jihar Kogi


Kakakin majalisar Wakilai Yakubu Dogara ya rantsar da Haruna Isa sabon wakilin da aka zaba daga jihar Kogi.

Kakakin majalisar ya rantsar da shi ya yin zaman majalisar na yau Laraba.

An zabi Isa ya yin zaben cike gurbin da hukumar zabe ta gudanar cikin watan Agusta a mazabar majalisar wakilai ta Lokoja/Koton-Karfe.Kuma ya lashe zaben ne a karkashin jam’iyar APC.

An gudanar da zaben domin cike gurbin da ya samu sakamakon mutuwar Umar Jibrin tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar wanda shine ke wakiltar mazabar.

Isa ya kayar da abokin karawarsa na jam’iyar PDP, Bashir Abubakar da ƙuri’u 26860.


Like it? Share with your friends!

-1
107 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like