Dino Melaye ya yabawa Buhari


Dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar yammacin Kogi,Sanata Dino Melaye ya yabawa shugaban kasa, Muhammad Buhari kan yadda ya gabatar da kasafin kudin bana.

Melaye na daga cikin yan majalisar da suka jeru suna yiwa shugaban sowa da tafi lokacin da yake fita daga zauren majalisar bayan ya gabatar da kasafin kudin wannan shekara.

Melaye ya raba gari da shugaban kasa, Buhari lokacin rikicin da ya dabaibaye majalisar kasa a shekarar 2015.

Ya zuwa karshen shugabancin Buhari zangon farko Melaye ya sauya sheka daga jam’iyar APC ya zuwa jam’iyar PDP inda ya sake lashe zabensa.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like