Diego Maradona ya mutu


Shararren dan kwallon kafar kasar Argentina, Diego Maradona ya mutu.

Maradona ya mutu sanadiyar bugawar zuciya makonni biyu kenan bayan da aka sallame shi daga asibiti.

Dan wasan ya bada gudunmawa sosai ga kasar Argentina har ta samu nasarar lashe gasar kofin duniya a shekarar 1986

An dai yi masa magani ne a asibiti bayan da ya samu kwararar jini a cikin kwakwalwarsa.

Tuni manyan kungiyoyin kwallon kafa suka shiga mika sakon ta’aziyar rasuwar marigayin.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like