Daya Daga Cikin Wadanda Aka Kwato Daga Hannun BokoHaram Ta Tsere Ta Koma Ga Mijinta Dan BokoHaram Matar wani kwamandan Boko Haram, Aisha, da aka ceto ta tsere daga gidansu da ke Maiduguri ta koma wajen mijinta dan Boko Haram da ke dajin Sambisa.

Kana ta tafi da yaron da ta haifa ma dan Boko Haram din mai suna Mamman Nur.

Ta arce ne bayan fitowa daga shirin gwamnatin tarayya na wayar musu da kai bayan an ceto su daga hannun Boko Haram.

Yar uwarta, Bintu Yerima, ta bayyana cewa Aisha ta kwashe kayayyakin ta ne bayan ta amsa wani kira a waya.

Tace:“Kafin ta tafi, ta amsa wayar wata mata wacce ke tare da ita a shirin. 
Matar tace sun koma dajin Sambisa”.
Bintu tace bayan arcewanta, Aisha ta ki amsa wayarta, a karshe ma kashe wayar tayi.

Wata masaniyar tunanin dan Adam, Fatima Akilu tace da ta samu labarin wasu yan mata sun koma wajen Boko Haram, ta lura da cewar wasunsu na son komawa saboda dadin da suke ji da kuma kunyar da suke ji cikin jama’a da kyama.

Comments 0

Your email address will not be published.

Daya Daga Cikin Wadanda Aka Kwato Daga Hannun BokoHaram Ta Tsere Ta Koma Ga Mijinta Dan BokoHaram 

log in

reset password

Back to
log in