Dariye zai shafe shekaru 14 a gidan yari


Wata babbar kotun birnin tarayya Abuja, ta yankewa tsohon gwamnan jihar Plataeu, sanata Joshua Dariye, hukuncin daurin shekaru 16 a gidan yari.

Dariye wanda sanata ne mai ci a yanzu zai yi zaman gidan yari na shekara 2 da kuma 14 a tare.

Alkalin kotun mai shari’a, Adebukola Banjoko bata bashi zabin biyan tara ba.

Tsohon gwamnan yaje kotun sanye da babbar riga mai launin shudi inda ya samu rakiyar iyalinsa, yan uwa da kuma abokanan siyasa.

A shekarar 2007 hukumar EFCC ta gurfanar da shi a gaban kotu inda take tuhumarsa da laifin almundahana da dukiyar al’umma.

Ana zarginsa da laifin karkatar da kudin asusun zai-zaiyar kasa mallakin jihar da yawansu ya kai naira biliyan ₦1.126.

Tsohon gwamnan ya karkatar da kudin ta hanyar yin amfani da wani kamfani wanda bashi da rijista mai suna Ebenezer Reitner Ventures wajen karkatar da kudaden.

Sati biyu da suka wuce kotun ta yankewa tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari.


Like it? Share with your friends!

2
57 shares, 2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like