Danjuma Goje ya janye daga takarar shugabancin majalisar dattawa


Danjuma Goje,sanata dake wakiltar mazabar Gombe ta tsakiya ya janye daga takarar da yake ta neman zama shugaban majalisar dattawa.

Goje ya kuma nuna goyon bayansa ga takarar sanata Ahmed Lawal.

Da yake magana da manema labarai bayan wata ganawa da shugaban kasa, Muhammad Buhari ranar Talata inda ya ce ya dauki matakin ne domin nuna girmamawa ga shugaban kasa da kuma jam’iyar APC.

Jagorancin jam’iyar APC da kuma shugaban kasa Buhari sun goyi bayan Lawan ya zama shugaban majalisar amma duk da haka abokan aikinsa biyu daga yankin arewa maso gabas wato Sanata Ali Ndume da Danjuma Goje sun nuna sha’awarsu ta jagorantar majalisar.

Da aka tambaye shi ko ya fuskanci matsin lamba kan ya janye daga takarar, tsohon gwamnan ya ce babu wata matsin lamba face a matsayinsa na dattijo dake da hankali ya gane cewa zabin dattawa da kuma girmama jam’iya ke gaba da komai.

Gwamnan jihar Kaduna,Nasir El-rufai da kuma mai bawa shugaban kasa shawarar kan harkokin majalisar dattawa, sanata Ita Enang na tare da Goje lokacin da yake ganawar da yan jarida.


Like it? Share with your friends!

1
82 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like