Dan takarar gwamnan jihar Kano karkashin jam’iyyar GPN ya gurfana a gaban kotu


Hukumar Yaki da Masu Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati EFCC ta gurfanar da, Abdulsalam Saleh Abdulkarim wanda akafi sani da AA Zaura dantakarar gwamnan jihar Kano a jam’iyar GPN, a gaban kotu.

Hukumar na zarginsa da aikata damfarar kudi da yawansu ya kai dalar Amurika miliyan $1.3.

Abdulkarim da kuma Ebere Nzekwe sun gurfana gaban mai shari’a Lewis Allagoa na babbar kotun tarayya dake Kano inda ake tuhumarsu da aikata laifuka tara ciki har da karbar kudi ta hanyar karya.

A cewar Jamman Al-Azmi mutanen da yake kara sun yaudare shi inda suka karbi miliyan $1.3 inda suka bashi tabbacin cewa za a zuba kudin a wata harkar kasuwanci.

Dukkannin mutanen biyu basu amsa laifin da ake tuhumarsu da shi ba.

Mai shari’a Allagoa ya bayar da belin mutanen kan kudi miliyan ₦100 da kuma mutumin daya da zai tsaya musu.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like