Dan bindiga ya harbi wani malamin coci a Faransa


Wani dan bindiga dadi a kasar Faransan ya harbi wani malamin cocin kibɗawa a birnin Lyon na ƙasar.


Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa maharbin ya tsere bayan da ya aikata laifin a ranar Asabar.


An harbi malamin cocin sau biyu da misalin ƙarfe 4:00 na yammacin ƙasar a daidai lokacin da yake shirin rufe coci.


Tuni dai jami’an agaji suka fara yi masa magani a cocin da aka yi harbin sakamakon raunukan da ya samu masu barazana ga rayuwarsa.
Ko a ranar Alhamis sai da aka kashe mutum uku a wani hari da aka kai da wuƙa a birnin Nice na ƙasar.


Hakazalika kwanaki kaɗan baya sai da wani mahari ya datse kan wani malamin makaranta a ƙasar bayan malamin ya nuna wa ɗalibansa wasu hotunan zanen ɓatanci da aka yi ga manzon Allah, Annabi Muhammad SAW.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 6

Your email address will not be published.

You may also like