A makon da ya gabata, kamfanin Twitter ya goge wani sako da Shugaba Muhammadu Buhari ya wallafa wanda ya ce ya saba ka’ida, su kuma hukumomin Najeriya suka dakatar da amfani da kafar sada zumuntar a ranar Juma’a, matakin da ke ci gaba da shan suka.

‘Yan majalisar na bangaren babbar jam’iyyar adawa ta PDP sun fice zauren majalisar ne don nuna rashin jin dadinsu bayan da shugaban majalisar Femi Gbajabiamila ya ki sauraren bukatar da Kinsley Chinda ya gabatar.

Chinda wanda ke wakiltar mazabar kananan hukumomin Obio/Akpor a jihar Rivers, jagora ne a tsakanin mambobin ‘yan PDP dake majalisar.

Ya nemi majalisar da ta umarci gwamnatin tarayya ta janye haramcin da ta sakawa Twitter yayin da majalisar ke bincike kan lamarin.

Sai dai a lokacin da yake yin tsokaci kan kalaman na Chinda, shugaban majalisar wakilan, Gbajabiamila, ya ce majalisar ta riga ta kammala tattaunawa kan wannan batu, saboda haka ba za saurare shi ba.

A cewar Gbajabiamila, daya daga cikin ka’idojin majalisar shi ne, ba za a yi muhawara kan wani batun da majalisar ta riga ta kammala magana akai ba.

Wannan ya sa ‘yan jam’iyyar ta PDP suka fice daga zauren, saboda abinda suka kira rashin adalci da aka nuna masu.

Jam’iyyar APC ce dai ke da rinjaye a majalisar ta wakilai mai mambobi 360.

Gabanin Chinda ya ta da wannan batu, shugaban majalisar ya umarci kwamitocin da ke kula da fannin sadarwa, shari’a da na al’adu, da su gudanar da bincike kan lamarin tare da mika goron gayyata ga Ministan yada labarai Alhaji Lai Mohammed, don ya bayyana a gaban ya yi mata bayan ikan dalilinsu na dakatar da Twitter