Babban bankin Najeriya CBN, ya ce dalilin da ya sa ya haramta sayar da dala da sauran kudaden kasashen waje ga masu hada-hadar canji a kasar shi ne, ana amfani da su wajen halalta kudaden haram.

Bankin na CBN ya kuma ce zai dakatar da ayyukan ba da lasisi ga masu neman bude kasuwancin canjin kudaden kasashen waje.

“Mun damu, saboda masu ayyukan canjin suna bari ana amfani da su wajen dabbaka ayyukian cin hanci da rashawa.” Gwamnan CBN Godwin Emefiele ya fada yayin wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin a ranar Talata.

Ya kara da cewa, “babu yadda za mu ci gaba da zura ido muna kallo ana wannan tabargazar a kasuwannin na canji.”

Emefiele ya ce daga yanzu, kudaden kasashen wajen za su rika tafiya kai-tsaye zuwa bankunan kasar.

Rahotanni sun ce tuni har farashin dala yah aura a ranar Talata bayan da babban bankin na Najeriya ya ayyana wannan sabon tsari.