Daliban jami’a 6 sun fada hannun yan sanda kan zargin aikata fashi da makami


Yan sanda a jihar Neja sun kama wasu daliban jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida dake Lapai, su shida kan zarginsu da aikata fashi da makami.

Ana zargin daliban da addabar yan uwansu ta hanyar fashi da makami a dakunan kwanan daliban dake makarantar.

Mai magana da yawun rundunar yansandar jihar,DSP Mohammed Abubakar ya ce an kama mutanen ne bayan da wani ya yi musu ihu.

Wakilin jaridar Daily Trust ya gano cewa cikin makonni uku da suka wuce yan fashi da makami sun kai jerin farmaki kan gidajen kwanan dalibai dake wajen jami’ar

A cewar DSP Abubakar daya daga cikin mutanen da ake zargi wani ya gane shi cikin yan fashin da suka shiga dakinsa ranar 22 ga watan Satumba.


Like it? Share with your friends!

2

You may also like