Dalibai Sun Koma Makaranta A Nijeriya, Sun Fara Shirin Zana Jarabawa


Rahotannni sun bayyana cewa an bude makarantun sakandire, firamare da kwalejojin kimiyya a fadin Nigeria, domin ci gaban da karatu.

Sharuddan da aka gindayawa makarantun a yayin budewa sune wanke hannuwa, amfani da makarin fuska, amfani da sinadarin kashe kwayoyin cuta da gwajin zafin jiki.

Babban sharadin shine tabbatar da bata tazara a tsakanin dalibai, malamai da ma’aikata a yayin da ake gudanar da ayyukan makarantar.

Wasu daga cikin makarantun jihar Lagos, domin ganin yadda makarantun ke bin sharuddan da aka gindaya masu.

Gwamnatin tarayya ta baiwa makarantun damar budewa, domin ba dalibai damar zana jarabawar kammala sakandire. Hakan na zuwa bayan shafe watanni makarantun na a kulle, sakamakon barkewar annobar korona.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like