Dakarun Sojojin Saman Nijeriya Sun Ragargaza Sansanin ‘Yan Boko Haram A Dajin Sambisa


Rundunar sojojin sama ta Operation LAFIYA DOLE, ta ragargaji ‘yan Boko Haram a dajin Sambisa da ke jihar Borno.

Kakakin rundunar sojin, Manjo Janar John Enenche, ya ce rundunar ta yi harbin ne ta sama, a bangarori 2, bangaren Sambisa da Gobara, inda yace sun yi amfani da salo na musamman don kai wa ‘yan Boko Haram din hari.

Ya ce sojojin sun yi harbin ne daidai wuraren da suke zargi.

Saboda sai da suka duba kuma suka yi nazari a wuraren da ‘yan ta’addan suka kafa daba, tukunna suka yi harbin. Hakan ya yi sanadiyyar kashe yawancinsu.


Like it? Share with your friends!

-1

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like