Dakarun Najeriya Sun Musanta Harin Da ISWAP Take Ikirarin Ta Kai Kan Sojojin Hadin GwiwaA cewar labarin wanda ake yayatawa a kafafen sadarwar Internet, mayakan ISWAP din sun kashe sojoji, tare kuma da kwace wasu makamai da kayan aikin soji a harin.

To sai dai wata sanarwa da kakakin rundunar ta MNJTF Kanal Muhammad Dole ya fitar, ta ce sam wannan labarin bai da ko kamshin gaskiya.

Sanarwar ta ce mayakan kungiyar ta ISWAP da ma Boko Haram na fuskantar ukuba ne sakamakon farauta da luguden wuta da dakarun rundunar ke yi musu, tare kuma da turjiya da suke fuskanta daga al’ummomin yankin na Tafkin Chadi.

Manjo Janar I.M. Yusuf, Babban kwamandan runfunar MNJTF

Manjo Janar I.M. Yusuf, Babban kwamandan runfunar MNJTF

“Wannan ne dalilin da ya sa kungiyar ‘yan ta’addan ta soma kitsa labaran kanzon kurege da yayata farfagandar karya, domin ci gaba da rike mayaka da magoya bayansu da ke kokarin kubuce musu” a cewar sanarwar.

Rundunar ta dakarun na hadin gwiwa ta tabbatar da kudurinta na ci gaba da fatattakar ‘yan ta da kayar baya, tare da manufar dawo da zaman lafiya da tsaro a yankunan.

Akan haka ne sanarwar ta bukaci al’ummar yankin na tafkin Chadi da ta yi watsi da labaran karya da ake yayatawa, na cewa an kai harin kan dakarun rundunar ta hadin gwiwa.


Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.