DA DUMIDUNINSA: Za A Mayar Da Sheikh Zakzaky Kurkukun Kaduna A Yau


Yau ne kotun jihar Kaduna ta ci gaba da sauraron shari’ar dake gudana tsakanin Gwamnati da Sheikh Zakzaky wanda suke tuhuman shi da wasu laifuka, tin bayan abinda yafaru a watan Disambar 2015 tsakanin su da rundunar sojojin Najeriya wanda yayi sanadiyar rasa daruruwan rayukan ‘yan Shi’a.

Zama na karshe da akeyi a farkon shekarar nan wanda koto ta bada umurnin abar Malamin ya yatafi kasar waje neman lafiya, wanda daga bisani tafiyar tayi kom-gaba-kom baya, inda Sheikh din yaki amincewa da tsarin da hukumar DSS sukayi masa yayin tafiyar wanda yace shiri ne na shirya masa wata manakisa.

Watanni 4 da dawowan sa. Azaman na yau alkalin dake kare Sheik Zakzaky ya nemi a dage zaman saboda yace; DSS sunki subari ‘yan uwa da lauyin Sheikh din su ganshi tin bayan dawowan, wanda lauyan Gwamnati yayi inkari haka yace; ko jiya wani lauyan gwamnati me sauna Sadau Garba ya ganshi.

Daga karshe Alkalin ya nemi da DSS su maida Sheik Zakzaky kurkukun Kaduna a yau sannan a bada lauyoyin sa dama su ganshi kowanne lokaci. Almajiran Shek Zakzaky naci gaba da gargadin Gwamnatin Najeriya kan cigaba da tsare Malamin nasu. A wani rahoton kuma an bayyana yanda jami’an tsaro ke harba tiyagas a duk inda sukaga gungun jama’a yau a Kaduna dede lokacin da ake sauraron Shari’ar. Daga karshe an dage shari’ar zuwa ranar 6/2/2020.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like