DA DUMIDUMINSA: Ta Tabbata An Dage Zaben Shugaban Kasa Da Za A Yi Yau Asabar


Biyo bayan awannin da ta dauka tana zama game da zaben 2019 a tsakiyar daren yau, daga bisani hukumar zaben ta dage zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu da za a gudanar a yau Asabar.

Shugaban hukumar Mahmud, ya bayyana cewa za a gudanar da zaben shugaban kasan ne a ranar 23 ga watan nan, wato mako mai zuwa.

Sai kuma zaben Gwamnoni da na ‘yan majalisun jiha za a gudanar da shi a ranar 2/03/2019 zuwa 09/03/2019

Rahotanni sun bayyana cewa an dage zaben ne bisa wasu matsaloli da suka ci karo da shirye-shiryen da INEC ta yi da kuma matsalar tsaro da ta taso. Haka kuma sauyin Kwamishinonin ‘yan sanda da aka yi na daga cikin matsalolin.

An yi iya bakin ƙoƙari domin ganin yiyuwar wannan zaɓen amma abun ya ci tura.


Like it? Share with your friends!

-1
95 shares, -1 points

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like