DA DUMI-DUMINSA: AN SASANTA ALI NUHU DA ADAM ZANGO


An sasanta tsakanin fitattun jaruman Kannywood guda biyu, wato Ali Nuhu da Adam A. Zango a Kano.

Hadaddiy kungiyar masu shirya finafinan Hausa ta kasa, MOPPAN, karkashin jagorancin Malam Abdullahi Maikano, ce ta yi wannan aiki a ofishin dattijon Kannywood kuma shugaban majalisar amintattu na kungiyar, wato Malam Abdulkarim Mohammed a yau Asabar.

Sakataren kungiyar MOPPAN reshen jihar Kano, Malam Salisu Officer, shi ne ya tabbatarwa da LEADERSHIP A YAU wannan bayani, ya na mai cewa, yanzu Ali zai janye karar da ya kai Adamu.


Like it? Share with your friends!

5
69 shares, 5 points

Comments 1

Your email address will not be published.

  1. Write a comment * Wannan Kuma Damuwan sune Ko sudaina Ko Karsu Daina Yasaura Nasu. Domin Kullum Suna Cikin Fada, Hakama Hadiza Gabon Da Amina Amal Suna Nasu Fadan, Dama SunaSon hankalin Mutane Ya Koma Kansune Kawai,

You may also like