Cutar shawara ta kashe mutane 8 a Bauchi


Gwamnatin jihar Bauchi ta sanar da cewa an samu mutuwar mutane 8 sanadiyar barkewar cutar shawara a karamar hukumar Ganjuwa ta jihar.

Shugaban hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar Bauchi, Dr. Rilwanu Muhammad ya fadawa manema labarai cewa mutanen sun mutu ne a makon da ya gabata.

“Lokacin da ake aikin yin allurar riga-kafi a makon da ya gabata an samu rahoton mutuwar mutane 8 sanadiyar wata cuta da ba a sani ba amma bayan an dauki jininsu an gwada sakamakon ya nuna cewa suna dauke da cutar zazzaɓin shawara.” ya ce.

Muhammad ya kara da cewa dukkanin mutanen an same su ne a karamar hukumar Ganjuwa.

Ya kara da cewa tuni gwamnatin tarayya ta yi shirin yin allurar riga-kafi a dukkanin kananan hukumomi 19 dake jihar.


Like it? Share with your friends!

-1

Comments 1

You may also like