Cutar Lassa Tayi Sanadin Mutuwar Mutum Daya A Jihar Adamawa


Da yammacin jiya talata ne gwamnatin jihar Adamawa ta tabbatar da mutuwar wata mata mai kimanin shekaru 29 da haihuwa sakamakon kamuwa da cutar lassa.

Kwamishinan lafiya ta jihar Farfesa Abdullahi Isa ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai a Yola, inda yace matar wacce ‘yar asalin karamar hukumar Numan ne ta kasance ta fara karban magani ne a Asibitin kudi dake Yola daga baya aka maida ita asibitin kwararru dake Yola “FMC”

Mutane hudu ne aka zarga da kamuwa da wannan cutar amma bayan da likitoci sukayi bincike sun tabbatar da cewa sauran ukun wadanda suka fito daga kananan hukumomin Yola ta arewa da Yola ta kudu da kuma Girei basuda wannan cutar kuma tuni aka sallamesu, Inji Kwamishinan

Isa ya kara da cewa ma’aikatar lafiya ta jihar Adamawa tayi tsayuwar mai daka wajan ganin ta dakile cutar baki daya a jihar, ya kuma kirayi al’ummar jihar dasu kasance cikin tsabtace muhallansu a ko da yaushe ta yadda bera bazai samu damar shigowa har ya shafa musu cutar ta lassa ba.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like