Cutar Lassa ta kashe mutum biyu a Gombe


Gwamnatin jihar Gombe ta tabbatar da cewa mutane biyu sun mutu sanadiyar kamuwa da cutar zazzaɓin Lassa kana ana cigaba da bincike kan wasu mutane biyar.

Kwamishinan lafiya na jihar, Dr. Ahmad Muhammad Gana wanda ya bayyana haka ranar Talata lokacin da yake jawabi yayin wani taron manema labarai ya ce ma’aikatar lafiya ta jihar tana jiran tabbacin daga dakin gwaje-gwaje kan halin da sauran mutanen suke ciki.

Ya ce mutum na farko da ya kamu da cutar an kawo shi ne baya cikin hayyacinsa daga karamar hukumar Bayo ta jihar Borno ranar 23 ga watan Janairu inda ya mutu a ranar a sashen da ake kebe mutane na asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya dake Gombe.

Dakta Gana ya kara da cewa mutum na biyu da aka samu da cutar ya fito ne daga jihar Gombe wanda shima ya mutu lokacin da ake masa magani a asibitin koyarwar dake Gombe.

Kwamishinan ya kara da cewa wani marar lafiya mai dauke da cutar dan asalin karamar hukumar Ibbi ta jihar Taraba an kwantar da shi a asibitin koyarwar ranar 16 ga watan Janairu inda aka yi masa magani ya warke tare da sallamarsa.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like