Cutar Korona ta kashe tsohon gwamnan Oyo, Ajimobi


Tsohon gwamnan jihar Oyo,Abiola Ajimobi ya rasu a wani asibiti dake Lagos.

Wata majiya dake cikin iyalin tsohon gwamnan ta fadawa wata kafar yada labarai cewa bai farfaɗo ba daga dogon suman da yayi a wani asibiti inda ake kula da lafiyarsa bayan da ya kamu da cutar Korona.

A cikin watan Maris ne ya zama mataimakin shugaban jam’iyyar APC a shiyar kudu maso yamma.

Tarihi ba zai manta da gwamnan ba kasancewarsa gwamna daya tilo da ya mulki jihar har sau biyu.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like