Cutar Korona: Shugaban kasar Ghana ya killace kansa


Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo- Ado ya shiga killace kansa har na tsawon sati biyu a matsayin matakin kariya duk da cewa an gwada shi baya dauke da cutar Korona a cewar gwamnatin kasar.

Hakan ya biyo bayan kamuwa da cutar da wani daga cikin mutanen da shugaban kasar ya yi mu’amala da su ya yi

Shugaban kasa Akufo-Addo ya fara killace kansa tun ranar Asabar kuma zai cigaba da aiki a fadar shugaban kasa dake Accara a cewar ministan yada labarai na kasar cikin wata sanarwa da ya fitar.

Kasar ta Ghana ta sanar da samun mutane 19,300 da suka kamu da cutar kuma tuni ta sassauta dokar kulle mai tsauri da ta saka.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like