Cutar amai da gudawa ta kashe mutane uku a Borno


Akalla mutane uku aka tabbatar sun mutu sakamakon sake barkewar cutar amai da gudawa a karamar hukumar Kukawa ta jihar Borno, kwamishinan lafiya na jihar, Haruna Mshelia ya bayyana haka.

Mshelia ya bayyana haka ne lokacin da Tedros Ghebrayesus shugaban hukumar Lafiya ta duniya WHO ya ziyarci ofishin bada agajin gaggawa na hukumar dake Maiduguri.

Ya ce an samu rahoton bullar cutar a Baga, Doron Baga,da kuma Kukawa.

Mshelia ya ce gwamnatin jihar tare da hukumar lafiya ta duniya WHO da kuma sauran hukumomi,mun rubanya kokarin da muke wajen shawo kan cutar a wuraren da ta bulla.

Ya kara da cewa watanni shida da suka wuce gwamanatin jihar ta gudanar aikin riga-kafin cutar a yankunan da abin ya shafa.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like