CP wakili shine kwamishinan yan sanda na jihar Kano har zuwa lokacin riyatarsa


Kamar yadda muka samu rahoto daga Daily Nigerian labarin da ake yadawa na cewar wai an canzawa kwamishinan yan sanda Muhammad Wakili wurin aiki daga Kano zuwa Zamfara ba gaskiya bane.

Rahoton ya nuna cewar CP wakili shine kwamishinan yan sanda a jihar Kano har zuwa yanzu kuma babu wata takarda da ta Iso gare shi zuwa yanzu

Saidai rahoton na nuni da cewar CP wakili zai yi ritaya ne nan da kwanaki biyu masu zuwa wato ranar 15th May 2019 bayan ya cika shekarun riyatarsa wato ya shafe shekaru 60 a duniya .

Don ana Kira ga Al’ummar jihar Kano da suyi watsi da duk wani Batu na canzawa kwamishinan yan sanda Muhammad Wakil wurin aiki.


Like it? Share with your friends!

-1
110 shares, -1 points

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like