Covid-19: Isra’ila ta kwashe yan kasarta daga Najeriya


Kasar Isra’ila ta fara kwashe yan kasarta daga Najeriya biyo bayan karuwar da ake samu ta masu dauke da cutar Coronavirus.

Wakilin jaridar Daily Trust ya gano cewa kasar ta Isra’ila ta fara kwashe yan kasarta a cikin jirgin saman kamfanin Air Peace.

Tun da farko jirgin sai da ya dauki wasu Isra’ilawa a filin jirgin sama na Lagos kafin ya sauka a Abuja ya kara daukar wasu.

Kasashe da dama musamman na Tarayyar Turai sun fara neman izinin basu damar debe yan kasarsu daga Najeriya saboda fargabar barkewar cutar Coronavirus.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like