Coronavirus:Gwamnan Anambra ya killace kansa


Gwamnatin jihar Anambra, ta tabbatar da cewa gwamnan jihar,Willie Obiano ya killace kansa.

Sakataren gwamnatin jihar,Farfesa Solo Chukwulobelu da kuma shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar,Primus Odili sune suka bayyana yayin taron manema labarai na hadin gwiwa ranar Litinin.

Manyan jami’an gwamnatin biyu, sun ce tun ranar 19 ga watan Maris ne gwamnan ya killace kansa.

Sun bayyana cewa gwamnan ya killace kansa ne bayan da ya yi cudanya da wasu mutane da ake zargin suna dauke da cutar.

Jami’an biyu ba suyi karin haske ba ko gwamnan ya yi gwajin kwayar cutar Coronavirus ba.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like