Coronavirus: Yan majalisar wakilai sun bayar da tallafin albashinsu na watanni biyu


Yan majalisar wakilai ta tarayya sun yanke shawarar bayar da gudunmawar albashinsu na tsawon watanni biyu domin taimakawa yakin da ake yi da cutar Coronavirus.

Shugaban majalisar, Femi Gbajamiala shine ya bayyana haka.

A cikin wani sakon fefan bidiyo da ya fitar ranar Talata, Gbajabiamila ya ce albashin da za a mikawa gwamnatin tarayya baya cikin gudunmawar kashin kai da yan majalisar za su yi.

Jaridar The Cable ta binciko cewa, albashin yan majalisar su 360 ya kama daga ₦600,000 zuwa miliyan daya.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like