Coronavirus ta halaka tsohon shugaban kasar Congo-Brazzaville


Tsohon shugaban kasar Congo,Jacques Joaquim Yhombi-Opango ya mutu bayan da ya kamu da cutar Coronavirus a kasar Faransa.

Yhombi-Opango ya mutu a ranar Litinin a wani asibiti dake birnin Paris yana da shekaru 80.

Tsohon shugaban kasar ya kasance yana fama da rashin lafiya kafin ya kamu da cutar Coronavirus a cewar dansa.

Ya jagoranci kasar Congo-Brazzaville daga shekarar 1977 zuwa 1979 lokacin da aka hanbarar da shi a wani juyin mulki da shugaban kasar na yanzu, Denis Sassou Nguesso ya jagoranta.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like