Coronavirus: Ko kun san sabon salon gaisuwar da shugabanni suka tsiro da ita?


Fadar shugaban kasar Tanzania ta wallafa wasu hotuna dake nuna shugaban kasar,John Magufili na gaisawa da kafa da daya daga cikin jagoran yan adawa.

Daya daga cikin hotunan ya nuna Magafuli da Maalim Seif Sharif Hamad suna gaisawa da kafa.

Sabon salon gaisuwar dai na daya daga cikin shawarwarin da ma’aikatan lafiyar kasar ta bayar na kare bazuwar cutar Coronavirus.

Kasashe da dama dai na cigaba da daukar matakan kariya daga cutar ta Coronavirus da ta samu asali daga birnin Wuhan na kasar China.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 28

Your email address will not be published.

You may also like