CORONA: Gwamnatin Tarayya Ta Gabatar Da Kudurin Bude Makarantu Ga Majalisar Dattijai


Karamin Ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba a yau Talata ya gabatar wa Majalisar Dattijai kasar kudurin ranar da za a sake bude makarantu a fadin kasar nan bayan lokaci mai tsawo da aka rufe makarantun saboda cutar Corona virus, kamar yadda Daily Nigeria ta ruwaito.

Ya gabatar da kudirin ne yayin ganawa da Kwamitin Majalisar Dattawa kan makarantun Firamare da Sakandare domin shirye-shiryen komawar daliban makaranta.

Zuwa yanzu gwamnatin kasar bata bayyana ranar da zaa bude makarantun ba.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like