CORONA: Gwamna Ganduje Ya Cire Dokar Kulle Gaba Daya A Jihar Kano


Rahotanni daga jihar Kano na cewa Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta janye dokar kulle da ta sanya a jihar don gudun yaduwar cutar Corona.

Bababban sakataren yada labarai na Gwamnan Kano Malam Abba Anwar shi ya bayyana haka a wata takarda da aka rabawa manema labarai.

Gwamnatin ta ce ragowar ranakun da ake kulle a Kano na Alhamis da Asabar da Talata an janye dokar gaba daya sakamakon yadda al’umma suke takura saboda dokar.

Ganduje ya yi kira ga al’ummar jihar Kano da su ci gabada bin matakan kariya da likitoci suka bayar.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like